A ranar Talata ne, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya rantsar da Sakataren gwamnatin jihar Awwal Bamanga Tukur, da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Dakta Amos Edgar.
Haka kuma gwamnan ya shaidi rantsar da kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati Barista Afraimu Jingi, babban jami’i mai binciken kudi Usman Ahmad, shugaban ma’aikata Shehu Isa Ardo da babban alkalin alkaliyar jihar Hafsat AbdulRahman ta jagoranta.
Da yake jawabi a lokacin amsar rantsuwar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana karfin gwiwa kan mutanen da ya basu mukaman.
Ya kara da cewa “ina fatan za ku yi aiki tare da fahimta, yarda da juna, da daukan matakan da za su ci gaba domin jama’ar Adamawa” inji Fintiri.
Da yake magana a madadin wadanda suka amshi rantsarwar Sakataren gwamnatin jihar Awwal Bamanga Tukur, ya godewa gwamnan da ya basu damar su yiwa jama’ar jihar aiki.
Ya kuma yi alkawarin gudanar da aiki bisa gaskiya da adalci kamar yadda yadda su ka amshi rantsarwa, ta yadda jama’a za su amfana da mukaman da’aka ba su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp