A yau Talata, aka rantsar da sabon shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, a wani ƙayataccen biki da aka gudanar a dandalin Black Star da ke Accra, babban birnin ƙasar.
Mahama, wanda ya taɓa mulkar Ghana, daga shekarar 2012 zuwa 2017, ya lashe zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Disamban 2024, da kashi 56.55 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen, inda ya kayar da Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia na jam’iyyar NPP mai mulki.
- Gwamnan Kano Ya Nemi A Rage Kuɗin Hajjin 2025
- Cece-kuce Kan Badaƙalar Kuɗaɗe A NNPCL: SERAP Ta Bukaci Mele Kyari Ya Yi Bayani
Wannan shi ne karon farko da aka samu mataimakiyar shugaban ƙasa, mace Farfesa Jane Nana Opoku Agyemang, a Ghana, inda a ɗayan bangaren kuma aka rantsar da ‘yan majalisar dokokin ƙasar.
John Dramani Mahma, da ya zo lokacin da Ghana, ke cikin matsin tattalin arziƙi tare da nauyin bashi, ya yi alƙawarin dawo da martabar tattalin arziƙin ƙasar ta hanyar tabbatar da gaskiya da riƙon amana da kuma yi wa babban bankin Ghana garanbawul.
Ya kuma ya sha alwashin yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul wajen rage kuɗaɗen da ake bai wa shugabanni da rage yawan masu muƙamin siyasa da daidaita albashin ma’aikatan gwamnati.
Cikin Shugabannin ƙasashe 21 da suka halarci taron bikin rantsarwar har da shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, da dai sauransu.