A yau Talata ne babban sakataren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta AL Ahmed Aboul Gheit, ya gana da mataimakin shugaban sashen yada bayanai na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban babban rukunin gidajen radio da talabijin na kasar Sin CMG mista Shen Haixiong, a birnin Alkahiran kasar Masar. Yayin tattaunawar, manyan jami’an biyu sun yi musayar ra’ayoyi game da batutuwan da suka shafi raya al’adu, da wasanni, da hadin gwiwar watsa shirye shirye da sauransu. Kaza lika, sassan biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa.
Har ila yau a dai jiyan, Ahmed Aboul Gheit ya gabatar da takardar shaida ta “wakilin sada zumunta tsakanin Sin da kasashen Larabawa ” ga CMG, don yaba kwazon sa a fannin ingiza abota tsakanin Sin da kasashen Larabawa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp