Jiya Lahadi 25 ga wata ne aka rufe bikin nuna fina-finai na tsibirin Hainan na kasa da kasa karo na 4, wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, da gwamnatin jama’ar lardin Hainan suka yi hadin gwiwar shiryawa a birnin Sanya na lardin.
Gaba daya, an samu fina-finai da yawansu ya kai 3761, daga kasashe da yankuna 116 dake fadin duniya, wadanda suka yi takarar lashe lambar yabo ta “Golden Coconut Award” ta bikin. A ciki, fina-finai da aka gabatar daga ketare sun zarta kaso 80 bisa dari.
Masanan fasahar fina-finai na kasar Sin, da na kasashen ketare su 13, sun gudanar da aikin tantancewa ta yanar gizo ko kuma a zahiri. A karshe, fina-finai 9 sun samu lambar yabon.
Yayin bikin, an nuna fina-finai guda uku da CMG ya gabatar, kuma an shiryawa masu sha’awar fina-finai ayyuka iri daban daban. Alal misali an nuna fina-finai a fili, an kuma nuna wasu fina-finan a fadin tsibirin. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)