A yammacin yau Asabar ranar 28 ga wata ne aka gudanar da bikin rufe gasar wasannin motsa jiki ta mutane masu bukata ta musamman ta Asiya karo na 4 a babban filin wasa na Olympics dake birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta mutane masu bukata ta musamman ta Asiya Majid Rashed, ya sanar da rufe gasar wasannin.
A cikin wannan gasar wasannin motsa jiki ta mutane masu bukata ta musamman ta Asiya a wannan karo, ‘yan wasan kasar Sin 439 ne suka halarci dukkan manyan wasanni 22 da kananan wasanni 390, inda suka samu lambobin yabo na zinare 214, da na azurfa 167, da na tagulla 140. Haka kuma sun karya matsayin bajimta na duniya har sau 13, na Asiya sau 35 da na wasannin motsa jiki ta mutane masu bukata ta musamman ta Asiya sau 136. (Mai fassara: Bilkisu Xin)