Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi ta dakatar da karatu nan take bayan zanga-zangar da ɗalibai bayan ‘yan fashi da makami sun kai hari ɗakunan kwanan ɗalibai.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da daddare a ɗakunan kwanan maza, inda ‘yan fashi suka jikkata ɗalibai biyu sannan suka sace muhimman kayayyaki.
- Jagora A ADC Ya Ƙaryata Zargin Atiku Ya Kankane Komai A Jam’iyyar
- Sadiq Umar Da Bello El-Rufai Sun Sayi Ƙungiyar Rancher Bees FC Ta Kaduna
Ɗalibai sun fito zanga-zanga, tare da rufe ƙofofin makaranta domin nuna damuwa da neman a ɗaukin mataki kan tsaro.
Amma daga baya wasu ɓata-gari suka shiga zanga-zangar, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka tarwatsa taron da barkonon tsohuwa.
Shugaban ƙungiyar dalibai, Haruna Umar, ya ce wannan ne karon farko da aka kai irin wannan hari a makarantar, kuma suna so a ɗauki mataki mai tsauri.
Rijistaran makarantar, Alhaji Kasimu Salihu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an rufe makaranta kuma an umarci ɗalibai su bar harabar makarantar har sai an bayar da sanarwa ta gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp