Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba, a ranar Laraba, ya ba da umarnin rufe makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Jalingo cikin gaggawa sabida tabarbarewar gine-ginen makarantun.
Kefas wanda ya kai ziyarar bazata makarantar da misalin karfe 12:00 na rana, ya kadu matuka game da halin da daliban suke ciki – mummunan halin da azuzun karatu da dakunan kwanan daliban ke ciki.
Gwamnan wanda ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar, Cif Gibon Kataps; kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Kizito Bonzina, da sauran jami’an gwamnati, ya nuna takaicinsa kan lamarin, ya kuma yi alkawarin gyara makarantar zuwa tsalelen ginin zamani.
Ya kuma ba da umarnin rufe makarantar cikin gaggawa domin gwamnatin ta samu damar fara aikin gyare-gyaren don inganta jin dadin daliban da malamansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp