Kungiyar masu sana’ar kiwon Kifi ta kasa reshen jihar Filato ta bayyana cewa, kashi hamsin daga cikin dari na masana’tun kiwon Kifi a jihar sun garkame masana’antun, saboda kalubalen da suke fuskanta.
Shugaban kungiyar masana’antun Johnson Bagudu ne ya sanar da hakan, wanda kuma ya ce, fannin kiwon Kifi a jihar na matsayin daya daga cikin fannin da ke samar da ayyukan yi ga jama’a masu yawa.
Ya ci gaba da cewa, fiye da leburori 4,000, ke aiki a masana’antun, sai dai ya yi nuni da cewa, a yanzu, saboda dimbin kalubalen da suka dabaibaye su a jihar, kashi hamsin na masana’antunn an rufe su, wasu kuma ba sa yin sana’ar yadda suke bukata.
Bagudun ya bayyana hakan ne, a hirarsa da manema labarai a jihar, sannan kuma ya ce, wasu daga cikin manyan kalubalen da masana’antun ke fuskanta sun hada da, tsadar abincin na kiwon Kifayen da tsadar magunguna kula da lafiyarsu da rashin samun kasuwa.
A cewar Bagudu, a baya jihar Filato ta kasance a kan gaba wajen samar da Kifi a kasar nan, amma a yanzu irin wadannna kalubalen sun janyo komai yay a tsaya chak ga sana’ar.
Bagudu, saboda haka ya ce, yanzu ya zama wajibi gwamnati ta kawo musu dauki, musamman ganin yadda fanin ke samar da dimbin ayyukan yi musamman ga matasan da ke a jihar.
“A baya jihar Filato ta kasance a kan gaba wajen samar da Kifi a kasar nan, amma a yanzu irin wadannna kalubalen sun jawo komai ya tsaya chik a sana’ar”.
Ya kara da cewa, wasu gwamnatocin jihohin da ke kasar nan, na tallfa wa masu sana’ar da ke a jihohinsu, inda ya bayar da misali da gwamnatin jihar Kano da ke tallafa wa masu sana’ar a jahar, musamman wajen sayen kwayayen da masana’antun jihar ke kyankyashe wa.
Shugaban ya sanar da cewa, kungiyar reshen jihar Filato, ba ta taba samun wani tallafi daga gun gwamnatin jihar ba, wanda ya kara da cewa, kungiyar ta mika sunayen ‘ya’yanta ga wasu hukumomi domin a tallafa musu, amma har yau babu wani tallafi da suka samu.
Ya ce, gwamnatin jihar na waiwaya masu sana’ar ce kawai idan aka samu aukuwar wata annoba, kamar ta murar tsintsaye saboda kauce wa shafar kiwon lafiyar al’ummar jihar.
“Kungiyar reshen jihar Filato, ba ta taba samun wani tallafi daga gun gwamnatin jihar ba, inda ya kara da cewa, kungiyar ta kuma mika sunayen ‘ya’yanta ga wasu hukumomi domin a tallafa masu, amma har yau babu wani tallafi da suka samu”.
Sai dai, Bagudu na da yakinin cewa, masu sana’ar na sa ran komai zai daidata, yadda za su fita daga cikin wannan kalubalen da suke fuskanta.