Hukumomi a jihar Uttar Pradesh ta kasar Indiya sun rusa gidajen musulmai da ake zargi da hannu a tarzoma a makon da ya gabata sakamakon kalaman batanci da wasu ‘yan jam’iyya mai mulki suka yi kan Manzon Allah SAW.
A yankin Kashmir na Indiya, ‘yan sanda sun kama wani matashi da ya yada wani faifan bidiyo yana barazanar fille kan tsohuwar mai magana da yawun jam’iyyar mai mulki wacce aka zarga da yin kalaman batancin, a wani bidiyon da aka yada a kafar YouTube. Amma daga bisani Hukumomi suka janye bidiyon.
Musulmi sun fito kan tituna a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a Indiya don nuna adawa da kalaman kyamar Musulunci da wasu mambobin jam’iyyar Bharatiya Janata ta Hindu mai ra’ayin kishin kasa ta Pira Minista Narendra Modi, suka yi.
An yi arangama tsakanin musulmi da mabiya addinin Hindu a wasu yankunan, a wani bangare kuma tsakanin masu zanga-zangar da ‘yan sanda a yankuna da dama.
‘Yan sanda a Uttar Pradesh sun kama mutane fiye da 300 da ake zargi da hannu a zanga-zangar.