Babban jami’in hukumar Premier League, Richard Masters ya ce an tsayar da ranar saurarar tuhumar Manchester City kan zargin karya dokar kasuwanci, to amma sai dai kuma Masters bai fayyace ranar da za a fara saurarar tuhumar da ake yi wa kungiyar ba.
Tuni dai aka kwashewa kungiyar kwallon kafa ta Eberton maki 10 bayan da aka samu kungiyar da laifin karya dokar kasuwancin kungiya, kuma laifi iri daya da na Manchester City.
- Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
Sannan a ranar Litinin an tuhumi kungiyar Nottingham Forest da laifin karya dokar cin riba a gasar firimiya da kasa samar da bayanai kan dorewar kasuwancin kungiya kuma
tun cikin watan Fabrairun shekara ta 2023 ake tuhumar Manchester City da karya doka 100, wadda har yanzu ba a gurfanar da ita don fuskantar hukunci ba.
A cikin watan Nuwamba aka yanke hukuncin cire maki 10 a Eberton, bayan da a watan Maris kwamiti mai zaman kansa ya samu kungiyar da laifi sai dai kungiyar ta daukaka karar hukuncin.
Ana tuhumar Manchester City da aikata laifukan tun daga 2009, kuma tun daga lokacin kungiyar ta dauki manyan kofuna guda bakwai amma wasu na cewa watakila a kori Manchester City daga Premier League zuwa Championship da karbe kofunan da ta lashe, idan aka samu kungiyar da laifi.
Ana kuma tuhumar kungiyar da kin bayar da hadin kai tun daga lokacin da Premier League ta fara tuhumar kungiyar a shekarar 2018, amma wasu rahotanni na cewa watakila a fara sauraren tuhumar a karshen shekarar 2024, amma ba a samu tabbaci ba daga mahukuntan Premier League ba sai dai ana ganin za a yanke hukunci kan Manchester City a 2025.