ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kalubalen Gwamnonin Da Suka Samu Nasara A Kotun Koli

by Bello Hamza, Abdullahi Muh'd Sheka and Hussein Yero and 1 more
2 years ago
Koli

LABARAI MASU NASABA

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

A ranar Jumma’a 12 ga watan Janairu 2024 ne kotun koli ta yanke hukuncin karshe a kan takaddamar da taso tun daga tokun sauraron kararrakin zaben gwamnoni a jihohin da suka hada da Legas, Kano, Bauchi, Filato da Zamfara inda kotun ta tabbatar da zaben da al’umma suka yi wa gwamnonin wadannan jihohin.

Ganin irin gwagwarmayar da aka yi fama da ita da yadda kan al’umma ya rarrabu, ya sa mutane da dama ke ganin akwai kalubalen da gwamnonin ke fuskanta a halin yanzu na hada kan al’umma ba tare da nuna bambancin siyasa ba.

  • Kasar Sin Ta Harba Kumbon Dakon Kaya Domin Aikewa Da Kayayyaki Ga Tashar Sararin Samaniya
  • ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano

Musamman a halin yanzu da ya kamata a fuskanci yi wa al’umma aiki, ganin mutane na fuskantar matsalolin tattalin arziki daban-daban da kuma matsaloilin tsaro da ke bukatar kulawa cikin gaggawa.

Kotun kolin ta yanke hukunci a kan zaben Babajide Sanwo-Olu na Legas, Abba Yusuf na Kano, Bala Mohammed na Bauchi, Caleb Mutfwang na Filato da kuma Dauda Lawal na Zamfara inda ta tabbatar da su a matsayin gwamnonin jihohinsu wanda hakan ya kawo karshen takaddamar da ke tattare da zaben gwamnonin da aka yi a shekarar 2023.

Kano

Batun Rusau Da Hada Kan Jam’iyya Ne A Kan Gaba

Akwai yiwuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf zai fuskanci manyan kalubale da suka hada da rikicin cikin gida wanda tun kafin a ci Talata da Laraba aka fara jin karar tasowarsa, wadannan kuma ba ya rasa nasaba da yadda wasu daga cikin masu taimaka wa gwamnan da kuma wasu kwamishinonin suke karbar umrnin daga babbar fadar Jam’iyyar ta NNPP, domin kamar yadda aka sani Gwamana Abba kafin wannan lokaci, shi ne mai taimakawa na musamman (PA) na Sanata Kwankwaso, hakan ta sa wasu dagan cikin masu rike da manyan mukamai har yanzu suke masa kallon PA.

Hakazalika, akwai gagarumar matsalaar da ta kamata tun yanzu Gwamna Abba ya fara tunanin yadda zai magance ta rusau da aka yi wa ‘yan kasuwa da wasu daidaikun mutane a Birinin Kano.

Wannan ba karamin kalubale ba ne idan aka yi la’akari da kasancewar Kano cibiyar ciniki kuma ga shi kai tsaye ‘yan kasuwar aka fara tabawa. Sai kuma batun korar ma’aikata wadda a wata majiya ta shaida cewa wannan matsala ce da ta tayar da matukar kura da ake ganin ita ce ta kai wani babban jami’in gwamnatin tafiya jinya a asibiti, kodayake an sallamo shi.

Hakazalika, akwai batun masarautu hudu da tsohon Gwamna Ganduje ya kirkira, kuma ake ganin suna cikin abubuwan da ba su kwanta wa wannan gwamnati a zuciya ba, sannan suna da tsarin abubuwan da suka ambata a lokacin yakin neman zaben da dole su aiwatar da su, kamar batun kawar da gine-ginen da suka ce ba a yi su bisa ka’ida ba kuma suka yi masu dirar mikiya. Ko shakka babu akwai bukatar sabon gwamnan ya yi wa wannan matsala kallon tsanaki domin gudun sake fadawa wani rikicin.

Ganin yadda Kanawa suka nuna wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kauna ya zama wajibi ya duba wasu daga cikin abubuwan da za su kara kyautata alakar gwmanatinsa da wasu sassan da suke ganin an saba masu a baya, kuma kamar yadda aka san al’adar siyasar Jihar Kano, akwai wasu rukunin al’umma kama da ga ‘yan Kasuwa, Malamai, iyayen kasa da masu fada aji daga cikin ‘yan siyasa da suke taka muhimmiyar rawa wajen nuna kyakkyawar alkiblar kowacce gwmanati, wannan tasa yake da muhimmacnin gaske gwamnan ya gaggauta yin la’akari da su domin taimaka wa gwamnatinsa. Duk da cewa dai jim kadan da yanke hukuncin kotun koli aka ji gwamnan ya sanar da kafa wani Kwamitin Dattijai da ya kunshi Tsoffin Gwmanonin Jihar Kano guda uku da suka hada da Malam Ibrahim Shekarau, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Zamfara

Mastalar Tsaro Da Bukatar Hada Kan Al’ummar Jihar

A yanzu haka hankalin Gwamna Dauda Lawal ya kwanta sakamakon tabbatar da shi da Babar Kotun Koli ta yi na cewa, shi ne zabben gwamna.

Daga kalubalen da Gwamna Dauda zai fuskanta, akwai daga bangaren ma’aikata,’yan siyasa da al’ummar gari-gari.

LEADERSHIP Hausa ta ji ra’yoyin mazauna Zamfara, kuma masana a kan zamantakeyar yadda Gwamna Dauda zai magance wadannan kalubalen da ke gabansa.

Kwamaret Ibrahim Kanoma Tsohon Ma’aikaci a Ma’aikatar yada labarai na Zamfara, ya bayyana cewa, babban kalubalen da ke gaban gwamna a bangaren ma’aikata shi ne dawo da darajar aikin.

Bangaren Siyasa kuma Malam Ibrahim Gada ya bayyana cewa, babban kalubalan Gwamna Dauda shi ne, Sanata Yari Abubakar, dan yadda a yanzu yake tafiyar da ‘yan siyasa da ba su tallafi da taimakonsu, lallai shi ma Gwamna Dauda sai ya kasance haka, tun da ga aiki yana ta zubawa sai kuma alheri ga ‘yan siyasa don yadda ake cikin yanayi a yanzu haka duk ayyukan da Gwamna Dauda zai yi idan bai hada da tallafin kudi da abinci ba lallai akwai matsala.

Don haka Gwamna Dauda ya duba da kyau ya bullo da wasu shiri na ba da tallafi ga al’umma don rage radadin halin da ake ciki, in ji shi.

Filato

Matsalar Tsaro Ita Ce Babbar Kalubalen Da Gwamnan Jihar Ke Fuskanta

Bayan tabbatar da Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, a matsayin gwamnan jihar ba kamar yadda kotun daukaka karar ta yi na dora dan takarar jam’iyyar APC, Nentawe Goshwe ba, babban kalubalen da yake fuskanta shi ne rashin tsaro wanda hare-haren da aka kai wa wasu al’ummomi lokacin bukukuwan kirsemeti suka fayyace irin matsalar tsaron da jihar ke ciki.

Baya ga sha’anin tsaro, ta fuskar siyasa ma Gwamna Caleb na fuskantar kalubalen hada kai da ‘yan majalisa da suka fito daga jihar wadanda suka fi yawa a jam’iyyar dawa ta APC a jihar. Dole Gwamnan ya samar da hanyoyin kara fahimtar juna da mutunta juna a tsakanin al’ummar jihar in har ana son samun ci gaba mai dorewa ci gaba da zamantakewa a jihar.

Koli
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Ne Afirka Ta Zamanantar Da Sufurin Jiragen Ruwa —Ɗantsoho
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Yadda Oyetola Ya Ƙaddamar Da Babban Taron Ƙungiyar  PMAWCA A Legas
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Lokaci Ya Yi Da Matasan Nijeriya Za Su Ƙwato Ƙasarsu — Kwamred Yahaya Abdullahi
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kamfanin Dangote Na Kara Karfafa Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Jihar Neja
Koli
Abdullahi Muh'd Sheka
+ posts Bio
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Sakamakon Matsin Lambar Jami’an Tsaro, ‘Yan Ta’adda Na Fuskantar Ƙarancin Abinci
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Kisan Gillar Mutum 7 A Kano: Sarakuna Da Malamai Da Iyaye Sun Nemi A Gaggauta Yanke Wa Waɗanda Ake Zargi Hukunci
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo
Koli
Hussein Yero
+ posts Bio
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Ɗan Takarar Sanata A Zamfara Ya Koka Kan Yi Wa Rayuwarsa Barazana
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Abdulaziz Yari Ya Bukaci Limamai Su Ƙara Addu’a Kan Yaƙi Da Ƴan Bindiga A Zamfara
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Matawalle Ya Buƙaci Magoya Bayansa Su Mara Wa Shugaba Tinubu, Gwamna Lawal Baya
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Majalisar Zamfara Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi Biyu Kan Zargin Almundahanar Kuɗaɗe
Koli
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Zaɓen Fidda Gwani Na Gwamna: Ba Za Mu Lamunci Kaƙaba Mana Ɗan Takara A Bauchi Ba – Mambobin APC
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Sanata Buba Ya Janye Daga Takarar Fidda Gwani Ta Gwamnan APC A Bauchi, Ya Zargi Cewa ‘Ɗauki Ɗaura Ake Yi Ba Zaɓe Ba”
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Koli
Rahotonni

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

May 17, 2026
Koli
Rahotonni

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

May 16, 2026
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada
Rahotonni

Almajiranci:Matsala Ko Maslaha

May 10, 2026
Next Post
Manzon Musamman Na Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Liberia

Manzon Musamman Na Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Liberia

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Ta Ƙara Yawan Man Da Take Tacewa Zuwa Ganga 700,000

Matatar Dangote Ta Ƙara Yawan Man Da Take Tacewa Zuwa Ganga 700,000

June 4, 2026
Ƴansanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga, Sun Kwato Shanu 25 A Sakkwato

Ƴansanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga, Sun Kwato Shanu 25 A Sakkwato

June 4, 2026
Takunkumin Amurka Ya Haifar Da Mummunan Tasiri Ga Tsarin Samar Da Kayan Latironi Na Duniya

Takunkumin Amurka Ya Haifar Da Mummunan Tasiri Ga Tsarin Samar Da Kayan Latironi Na Duniya

June 4, 2026
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi

June 4, 2026
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

June 4, 2026
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna

Gwamna Sani Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan Ɗaya Kan Tallafin Ɗalibai A Kaduna – Kwamishina

June 4, 2026
Sin Ta Ware Kudi Har Yuan Biliyan 99.9 Domin Tallafawa Kula Da Lafiyar Yara A 2026

Sin Ta Ware Kudi Har Yuan Biliyan 99.9 Domin Tallafawa Kula Da Lafiyar Yara A 2026

June 4, 2026
Tasirin Nasarar Da Kasar Sin Ta Cimma A Fannin Kakkabe Matsanancin Talauci

Tasirin Nasarar Da Kasar Sin Ta Cimma A Fannin Kakkabe Matsanancin Talauci

June 4, 2026
Sabbin Ra’ayoyin Ci Gaba: Manufofin Zamani Na Zamanantarwa

Sabbin Ra’ayoyin Ci Gaba: Manufofin Zamani Na Zamanantarwa

June 4, 2026
Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba

Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba

June 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.