A shekarar 2023 kadai, an sace wayoyi kimanin 83,545 a kasar Ingila kamar yadda rahotan hukumar ‘yansandan ƙasar ya bayyana.
Wani rahoto da kafar yaɗa labaru ta TRT ta Turanci ta wallafa, ya nuna yadda ake satar waya a kasar Ingila duk bayan minti shida (6).
- Rikicin Masarautar Kano: Sarki Bayero Ya Fara Bayyana A Bainar Jama’a A Kano
- Kotu Ta Wanke Tsohon Dogarin Bukola Saraki Kan Zargin Biliyan ₦3.5b
Rahotan ya bayyana yadda ake satar wayoyin ta hanyar amfani da kekuna masu amfani da lantarki da baburan tsere da kuma amfani da keken tsere wajen sace wayoyin.
Baya ga haka, rahoton ya bayyana yadda ake amfani da takarda wajen naɗe wayar (A wuraren zaman jama’a da kasar ke tanada), da kuma zare wayoyin a cikin jaka, da kuma amfani da makami wajen ƙwace wayar.
Rahoton ya nuna yadda wayoyin da aka sace ake fitar da su daga kasar tare da yin ƙasuwancinsu a kasashen ƙetare.
Wani wanda aka sace masa waya a kasar ingilan, ya bayyanawa kafar TRT din cewa “Bayan wani lokaci, kamar kwana hudu da sace wayar, dana bincika sai naga wayata a kasar China a yankin Shenzhen”
Binciken kafar TRT din ya nuna mafi ya yawa daga wayoyin da aka sace an fi siyar dasu a kasashen nahiyar Asiya.