Ƙungiyar YALI Network ta Kano ta kai tallafi ga mazauna yankin Gambaru na Maiduguri da ambaliyar ruwa ta shafa, inda ta raba kayan tallafi da suka haɗa da tufafi, da takalma, da gidajen sauro, da huluna, da kayan tsafta sama da guda 2,000.
Wannan shiri, ƙarƙashin jagorancin Barnabas Adesina tare da Barrister Abba Shuibu, ya mayar da hankali kan wayar da kai, da tattara kayan tallafi, da raba su daga Kano zuwa al’ummar da abin ya shafa.
- Ya Kamata A Dakatar Da Duk Wasu Wasanni A Sifaniya Saboda Ambaliyar Balencia – Ancelotti
- NEMA Ta Raba Kayan Tallafi Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kaduna
Yayin rabon tallafin, Barnabas Adesina ya bayyana cewa,
“Wannan yunkuri wata hanya ce ta nuna alhi da haɗin kai da ‘yan uwammu da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno.”
Ibrahim Aliyu Izege, wakilin koordinator na YALI a Jihar Borno, ya gode wa YALI Kano Hub bisa tallafin da ya bayyana da cewa,
“Wannan shi ne shugabanci na matasa tare da haɗin kai wajen tallafawa al’umma, musamman a lokacin da sanyi ke karatowa, wanda mata da yara ke bukatar taimako sosai.”
Shugaban ƙungiyar raya al’ummar Gambaru, Ali Yerima, ya bayyana godiyarsa inda ya ce, “Muna godiya ga YALI bisa wannan taimako. Allah ya saka musu da alheri kan wannan kyauta da ta kawo fata da sauki a garemu.” Wannan matakin ya jaddada ƙarfin matasa wajen hidima ga al’umma da kuma haɗin kai wajen magance ƙalubalen da ake fuskantar waɗanda suke cikin hali na rashin galihu.