A jiya Litinin ne aka zabi kasar Sin a matsayin mamba a hukumar harkokin sadarwa ta kasa da kasa ko ITU, wadda ke karkashin MDD.
Kaza lika an zabi daraktan cibiyar lura da harkokin kafofin Radio na kasar Sin Cheng Jianjun, a matsayin sabon mamba a sashen ITU mai lura da dokokin ayyukan Radio, zuwa tsawon shekaru 4 masu zuwa.
Ana gudanar da taron manyan wakilan kasashe mambobin ITU na shekarar nan ta 2022 ko PP-22, a birnin Bucharest na kasar Romania, tsakanin ranakun 26 ga watan Satumbar da ya gabata zuwa 14 ga watan Oktoban nan.
Cikin jawabin da ya gabatar game da manufofin kasa a ranar 27 ga watan Satumba, jagoran tawagar kasar Sin, kuma mataimakin ministan masana’antu da harkokin fasahar sadarwa na Sin Zhang Yunming, ya ce Sin na nacewa manufar samar da ci gaba mai la’akari da yanayin al’umma, tana kuma taka rawar gani wajen bunkasa samar da ababen more rayuwa da ake bukata a fannin masana’antun sadarwa.
Jami’in ya ce karkashin wannan manufa, an fadada hanyoyin samar da sadarwa, an hade sassa masu nasaba da hakan, kana an bunkasa kirkire-kirkire a fanni. Kaza lika hakan ya ba da damar zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannonin yada bayanai da sadarwa.
A hannu guda kuma, Sin a shirya take ta yi aiki tare da sauran kasashe, wajen karfafa bincike da samar da ci gaba, da karfafa hadin gwiwar masana’antu a bangaren fasahohin zamani kamar fasahar 5G, tana kuma ingiza cudanyar dukkanin sassan masana’antun sadarwar zamani na kasa da kasa, ta yadda karin al’ummun duniya za su ci gajiya daga ci gaban fannin. (Saminu Alhassan)