An saki wani dan kasar Amurka wanda aka yi kuskuren daurewa a gidan yari na tsawon shekara 28 a Missouri bayan zargin sa da laifin kisa, duk da ya sha musantawa.
A ranar Talata ne wani alkali Dabid Mason a kotun St Louis, ya yanke hukuncin da ya wanke mutumin mai suna Lamar Johnson, mai shekara 50.
- Abin Da Ya Sa A Daminar Da Ta Gabata Masara Ta Yi Tsada -Shugaba
- Tinubu Ya Isa Guinea-Bissau Domin Taron ECOWAS, Ya Ziyarci Sojojin Nijeriya
Alkalin ya ce ya yanke hukuncin ne bayan wasu shaidu biyu sun gabatar da gamsassun hujjoji da ya yadda da su da kuma suka nuna cewa mista Johnson ba shi da laifi.
An yanke masa hukunci ne bayan da aka zarge shi da laifin kashe wani mai suna Marcus Boyd a shekarar 1994.
Magoya bayan mista Johnson sun yi ta sowa da murna da kuma tafi lokacin da kotu ta sanar da wanke shi.
“Wannan abin farin ciki ne,” in ji mista Johnson, bayan barin cikin kotun.
A bara ne wani babban alkali, Kim Gardner, ya shigar da kara inda yake bukatar a saki mista Johnson bayan kammala binciken wata kungiya da ya nuna mista Johnson ba shi da laifi.
Bayan hukuncin da aka yanke a ranar Talata, lauyoyin mista Johnson sun soki ofishin babban attoni janar na jihar da ya bukaci a ajiye shi a gidan yari.
‘Ofishin bai daina cewa Lamar ba shi da laifi ba, inda ma ba su damu ba ko da ya mutu a gidan yari,’’ in ji lauyoyin mista Jonson a cikin wata sanarwa da suka fitar.
Mai magana da yawun ofishin attoni janar din ya bayyana a cikin wani sako cewa ba zai dauki wani karin mataki ba kan lamarin.
“Ofishinmu ya kare doka ne sannan kuma ya yi aiki domin tabbatar da an yi aiki da ainihin hukuncin da kwamitin lauyoyi ya yanke, bayan aiki da hujjojin da aka gabatar,’’ in ji sanarwar.
Wasu mutane biyu ne rufe da fuskokinsu suka harbe Marcus Boyd a gaban gidan mista Johnson a watan Oktoban 1994.
Mista Johnson ya sha nanata cewa ba ya gida a lokacin da aka far wa Marcus Boyd tare da kashe shi.
Alkali Mason ya yanke hukunci ne bayan da wani shaida ya soki bahasin da ya bayar, inda wani fursuna ya fadi gaskiyar cewa shi tare da wani mutum mai suna Phil Campbell suka harbe Boyd.
Tun da farko a zaman jin karar, Campbell ya amsa cewa yana da laifi, amma ya roki a sassauta masa hukunci, inda aka yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari.