Har yanzu noman Masara a kasar nan, musamman a arewa maso yamma suna yin noman ta da tsadar gaske.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar manoman Masara don samun riba na yankin arewa maso yamma Alhaji Adamu Muhammad Makarfi ya sanar da cewa, a kakar noman bana.
- GORON SALLAH
- Amsar Xi Jinping Ta Ba Duniya Damar Fahimtar Tsarin Binciken Hada-hadar Kudin Na Kasar Sin
Har yanzu noman Masara a kasar nan, musamman a arewa maso yamma suna yin noman ta da tsadar gaske.
Adamu a hirarsa da Leadership Hausa a kaduna yace, sabin yadda ake sayar da takin kan naira 5,000 a baya, a bana farashinsa ya ninka, inda ya ce, hatta magungunan feshi na kwari ko na kashe Ciyawa da kudin kwadago, kudaden su sun karu.
Ya ci gaba da cewa, haka ambaliyar ruwan sama da aka samu a wasu jihohin kasar nan kamar su, Zamfara, Sokoto, Jigawa, Katsina kaduna da wasu jihohin duk an samu wannan iftila’in, inda hakan ya janyo wa manoma yin asara.
Ya kara da cewa, “ A matsayi na, na manomi mu bukatar mu ba wai a sayar da amfanin gona da tsada a kasar nan ba, amma duk da haka, ba za mu so ace manoma sun yi asara ba, domin asarar manoma, asara ce ga kasa baki daya”.
Ya yi nuni da cewa, domin duk ida aka ce manomi ya yi noma kuma ya fadi, babban abinda ake jin tsaro, musamman manyan manoma da yawancin su suke yin noman don riba in sun fadi akwai matsala domin akasarin suna ciwo bashi ne a banki domin yin noma da kuma kudin ruwan da ake dora masu, asarar za ta yi masu yawa.
Adamu ya ci gaba da cewa, idan manyan manoma ba su yi noma ba a kasar nan, za samu karancin abinci, inda ya ce, hakan ne ya sa zaka ga ana yin kira aje a sawo abinci daga ketare, in an sawo abincin daga ketare, Nijeriya za ta iya yin asara mai yawa domin hakan zai iya dfurkusar da tattalin arzikin kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, misali an je an sawo tan miliyan biyu na Masara don shigo wa da shi cikin Nijeriya, sai an kashe kusan naira tiriliyan daya, inda ya kara da cewa, a kasar nan , ban da sauran amfanin gona kasar nan na bukatar akalla tan miliyan ashirin.
Ya ce, in har za a sawo Masara a kasar waje ba a noma a kasar nan ba, akalla za mu yi asarar zunzurutun kudi kamar naira tirilyan goma, inda ya yi nuni da cewa, idan ba a baiwa manoman kasar taimakon da ya dace, ba karamar matsala ce za ta auku ba.
Ya yi kira musamman ga gwamnatin tarayya, gwamnatin jihohi da na kananan hukumomi su mayar da hankali kan bunkasa noman rani, inda ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi a samar da kyakyawan tsari, amma idan ba a yi hakan ba, bamu san irin abinda zai faru a kasar nan ba.
Da yake yin tsaokaci kan tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi na dakile ‘yan kasuwa na kasar waje zuwa gonakan manoman kasar nan don sayen amfanin gona da suka noma kai tsaye, Makarfi ya ce, wannan tsarina bin yaba wa ne, sai ya sanar da gwamnatin ta makaro domin tun tuni ya kamata ace an yi irin wannan tsarin.