An saki dubban fursunoni a fadin Nijeriya daga gidan yari a kokarin da ake na magance cunkoso.
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya ce gwamnati ta amince da sakin fursunoni 4,068 daga cikin 80,804 da ke cikin gidajen gyara hali 253 a fadin kasar nan, wadanda ake tsare da su a gidan yari saboda sun kasa biyan tara.
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Hyacinth A Matsayin Gwamnan Benuwe
- Mutum 547,774 Ne Suka Cike Aikin Dan Sanda, Mako 1 Ya Rage Kafin Rufe Shafin Daukar Aikin
Kakakin ma’aikatar, Ajibola Afonja ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa fursunonin wadanda tarar su ba ta wuce naira miliyan daya ba ne kawai aka zaba tare da sakin su.
Matakin dai ya kasance wani mataki na yunkurin shugaba Bola Tinubu wanda da aka zaba a farkon wannan shekarar na ganin an kawar da cunkoson gidajen yari a Nijeriya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce gidajen yarin Nijeriya na da cunkoson jama’a na kashi 147 a maimakon 100, kuma wadanda ake tsare da su na iya jiran shekaru da dama kafin su samu damar bayyana a kotu.
An jima ana kiranye-kiranye ga gwannatocin baya na Nijeriya kan duba yiwuwar rage cunkoson fursunonin a gidan yarin.
A baya kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi barazanar maka gwamnatin Nijeriya a kotu kan take wasu hakokki na fursunonin da ake tsare da su.