Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayar da tabbacin cewa an kubutar da daliban da aka sace a makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kuriga, karamar hukumar Chikun.
A safiyar ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka mamaye makarantun firamare da sakandare inda suka yi awon gaba da wasu dalibai 287.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya sake jaddada kiransa na kafa ‘yan sandan jihohi.
Gwamnan ya ce, samar da rundunar ‘yan sandan za ta taimaka wa kokarin jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi Jama’a a fadin kasar nan.
“Na yi wa shugaban kasa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro bayanin halin da daliban Kuriga ke ciki, kuma na samu kwakkwaran tabbaci cewa ana daukar dukkan matakan dawo da daliban,” cewar Sani.
“Za a kafa kwamitin tsaro a Kuriga, wanda za a samu mambobi daga manyan masu ruwa da tsaki a yankin Kuriga, da hukumomin tsaro, da kuma gwamnatin jihar.
“Zan bukaci babban hafsan hafsoshi da a kafa sansanin soji a Kuriga domin karfafa tsaro a yankin.
“Abunda ya faru a Kuriga mara dadi ya kara karfafa matsayin mu na goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi. Inji Sani.
Uba Sani na kan gaba wajen yunƙurin samar da ‘yan sandan a jihohi.