Ragowar ɗalibai da malamai da aka sace daga makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke Papiri, a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja, sun samu ’yanci, kamar yadda majiyoyin tsaro da na al’umma suka tabbatar. Wannan na zuwa ne bayan shafe makonni ana fafutukar ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Wata majiya daga ɓangaren tsaro ta ce waɗanda aka sako su ne rukuni na ƙarshe daga cikin mutanen da aka sace a harin da aka kai makarantar a ranar 21 ga Nuwamba, koda yake ba a bayyana ainihin adadinsu nan take ba. ’Yan bindigar sun kai harin ne da asubahin safiya, inda suka ratsa ɗakunan kwanan ɗalibai suna kwashe mutane kafin su nufi dajin da ke kusa.
- Charles Onunaiju: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Sanya Sabon Ci Gaba A Nijeriya
- Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
Tun da farko, an sako kusan mutum 100 daga cikin waɗanda aka sace a ranar 8 ga Disamba, yayin da aƙalla ɗalibai 50 suka tsere da kansu a lokacin harin. Wannan ya rage yawan mutanen da ke hannun masu garkuwar kafin sakin su na ƙarshe da aka samu yanzu.
Majiyoyi sun ce ana jigilar waɗanda aka sako zuwa Minna, babban birnin jihar Neja, domin duba lafiyarsu tare da haɗa su da iyalansu. Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Neja ba su fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba.













