An sallami mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo daga asibiti a jihar Legas bayan samun nasarar yi masa tiyata da aka yi a satin da ya wuce.
Babban likitan mataimakin shugaban Kasa, Dakta Nicholas Audifferen, a cikin wata sanarwa, ya ce: “An kwantar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a asibitin Duchess International a Legas, a ranar Asabar da ta gabata, 16 ga Yuli, 2022, saboda dalilai da yawa.
- NNPP Ga Buhari: Ka Sanya Dokar Ta Baci A Jihohin Arewa 5
- ‘Yan Bindiga Sun Saki Karin Mutane 4 Daga Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-KadunaÂ
“Ya samu karaya a damansa. An yi masa tiyata ba tare da wata matsala ba.
“An kwantar da shi tsawon kwanaki bakwai, yanzu ya far murmurewa. An sallame shi kuma yanzu yana samun sauki.
“Farfesa Osinbajo ya gode wa daukacin ma’aikatan asibitin karkashin jagorancin babban jami’in gudanarwa, Dokta Tokunbo Shitta-Bey da daraktan likitoci, Dokta Adedoyin Dosunmu-Ogunbi bisa kwarewa da ingancin kulawa da ya samu a wajensu.
“Mataimakin shugaban kasa ya kuma yaba tare da fatan alheri ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ‘yan Najeriya daga kowane bangare da ma kowa da kowa kan fatan alheri da samun sauki da aka masa.
“Mataimakin shugaban kasa zai ci gaba da murmurewa a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.”