Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ce ta samu afkuwar gobara 258 a cikin watanni uku a sassa daban-daban na jihar.
Daraktan hukumar Alhaji Hassan Muhammed ne, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai (NAN) a ranar Talata a Kano.
- Joe Biden Ya Ayyana Aniyar Sake Tsayawa Takarar Shugabancin Amurka
- APC Ta Kori Dan Takarar Gwamna Da Zababben Sanata A Jihar Taraba
Mohammed ya ce an samu labarin faruwar lamarin a kamfanoni, gidaje, shaguna, gidajen mai, kasuwanni, gidajen kiwon kaji, motoci da sauransu.
“Yawancin faruwar gobarar ta faru ne sakamakon rashin amfani da na’urorin lantarki yadda ya dace da cunkoson wutar lantarki, da cusa abubuwa da yawa a cikin mashin guda daya da kuma amfani da wayoyin wutar lantarki na jabu da marasa inganci,” in ji shi.
Muhammed ya shawarci jama’a da su daina ajiye man fetur a gida, mai a janareta a lokacin da yake kunne, da kuma gyara gurbacewar iskar gas a gida.
Daraktan ya kuma bukaci mazauna jihar da su rika kashe gas da tukunyar girki a duk lokacin da ba a amfani da su kuma su daina amfani da maganin sauro na hayaki a kusa da dakin girki.