Magoya bayan Bayern Munich da Galatasaray sun yi arangama da sanyin safiyar Talata a daya daga cikin manyan mashahuran wuraren shakatawa a santanbul gabanin wasansu na gasar zakarun Turai.
Kafofin yada labaran Turkiyya sun ce magoya bayan Jamus hudu da wani dan kasar Turkiyya daya sun samu raunuka kadan.
- Gwamnan Zamfara Zai Binciki Badakalar Miliyan 774 A Hukumar Alhazai Ta Jihar
- Yadda Aka Yi Walimar Saukar Alkur’ani Ta ‘Yar Abba El-Mustapha
Hotunan kyamarori kan titi sun nuna yadda magoya baya ke jefa kujeru da kananan alluna daban-daban a kan babbar hanyar gundumar Beyoglu da ke birnin Santanbul.
‘Yansanda sun shiga tsakani lokacin da magoya baya suka fara jifa a daya daga cikin shagunan sayar da kayayyaki na birnin na Santanbul.
Kamfanin dillancin labaran IHA ya bayyana cewa, magoya bayan Munich 70 da na Galatasaray 30 ne suka shiga rikicin.
Bayern ta buga wasanni 36 na gasar zakarun Turai a matakin rukuni ba tare da an doke ta ba, kuma tana rukunin A matsayi na daya.
Galatasaray ita ce ta biyu a rukunin kuma ta samu nasara a kan Manchester United a wasan su na karshe da suka buga kafin a je hutun wasannin kasa da kasa.