Hukumar tsaro ta kasa (NSC) ta bayyana gamsuwarta da matakan tsaron da aka dauka a fadin kasar nan, inda ta ce, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar kamar yadda aka tsara, cikin kwanciyar hankali.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ne suka bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa a ranar Laraba.
A cewarsu, ‘yan majalisar zartaswar sun nuna gamsuwarsu da lamarin, inda suka amince cewa shirin ya yi kyau.
Malami ya ce, babban hafsan hafsoshin tsaro, hafsoshin tsaro uku, Babban sufeton ‘yansanda da shugabannin sauran hukumomin tsaro sun bayyanawa majalisar zartaswar shirye-shiryensu na samar da matakan tsaro da suka dace domin gudanar da zaben a ranar Asabar.
Ya ce, sabida wannan tabbacin ne, majalisar ta ba da umarnin gudanar da zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsara.