Ma’aikatan INEC ba su iya rarraba kayan zaben gwamna da ‘yan majalisun jihohi a kan lokaci a garin Kafin Madaki da ke karamar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi ba.
Wakilinmu ya ziyarci cibiyar da ake rarraba kayan zabe a Center Primary School da ke Kafin Madaki da karfe 9am inda ya tarar da cewa a lokacin ne ake rarraba kayan zaben lamarin da ke nuni da cewa ba za a iya fara aikin zaben a kan lokaci ba.
- Zaben Gwamnoni: Na’urar BVAS 22 Sun Yi Batan-Dabo A Ribas
- Tsokaci A Kan Sabanin Da Ake Samu Wurin Mu’amala
Tunin dai mutane masu jefa kuri’a suka fara korafin rashin zuwan masu aikin zaben a kan lokaci.
“Damuwarmu shi ne idan har sai karfe 9am za a raba kayan zabe, har yanzu masu aikin suka je duk rumfunan zabe don fata aikin. Ya kamata INEC ta magance wannan matsalar domin inganta aikin zabe, mun fito tun karfe 8 amma ga mu ba mu San lokacin fara aikin jefa kuri’a ba,” Malam Muhammad Adamu, wani mai zabe a Kafin Madaki.
Sannan wakilinmu ya nakalto cewa wasu masu aikin wucin gadi wa INEC na karbar kayan zabe da tafi zuwa rumfar da za su yi aiki ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba.