An samu karuwar sayayya cikin kwanaki 8 na hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na bana da ake kira “Super Golden Week”, inda aka ga karuwar sayayya a fannoni daban-daban.
Alkaluma daga ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin sun nuna cewa, muhimman bangarorin sayar da kayayyaki da na samar da abinci, sun bada rahoton samun karuwar sayayya da kaso 2.7 yayin hutun.
Kuma daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Oktoba, yawan masu zirga-zirga a hanyoyin tafiyar kafa masu kantunan sayayya da manyan wuraren hada-hadar kasuwanci 78 da ma’aikatar ta bibiya, ya karu da kaso 8.8 kan mizanin shekara-shekara, kuma kudin shigarsu ya karu da kaso 6.
Bugu da kari, an samu sabon yanayin sayayya yayin hutun, inda bangarorin da suka shafi kayayyaki masu kare muhalli da na fasahohin zamani da kayayyakin kwalliya masu sigogi na zamani da na gargajiya na Sin, suka kara samun tagomashi. Alkaluma sun nuna cewa, sayayyar abincin da aka samar ba tare da sinadarai na zamani ba ta karu da kaso 27.9 kan mizanin shekara-shekara, sayayyar na’urorin amfanin gida ta karu da kaso 14.3, yayin da ta riguna masu sigogin zamani da na gargajiya na Sin, ta karu da kaso 14.1. (Fa’iza Mustapha)