A yau, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar a wani taron manema labarai cewa, a cikin watanni 11 na farkon shekarar da ta gabata, jarin da ba na zuba kudi kai tsaye ba na kasar Sin a kasashen waje ya karu da kashi 12.4 cikin dari a mizanin shekara-shekara, yayin da kuma kudaden sabbin kwangilolin ayyukan da ake gudanarwa a kasashen waje suka karu da kashi 13 cikin dari a mizanin shekara-shekara.
Bugu da kari, a shekarar 2024, kasar Sin ta ci gaba da kara yawan abokan huldar cinikayya cikin ‘yanci, kana yawan cinikin da ake yi ta wannan fuskar ya zarce kashi 1 bisa 3. Har ila yau, kasar Sin ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki tare da kasashen Afirka 23.
Kazalika, ma’aikatar cinikayyar ta ce, cinikayyar kayayyaki na kasar Sin tare da sauran abokan hulda na shawarar Ziri Daya da Hanya Daya sun kai na yuan tiriliyan 22.1, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.07 a shekarar 2024. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)