Yayin da Sinawa suke maraba da hutu mai tsawo na farko bayan na kwanaki 7 da suka yi yayin bikin bazara a watan Junairu, an samu yawaitar tafiye tafiye da tagomashi a bangaren yawon bude ido.
A cewar hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin, yawan fasinjojin da suka bi jiragen kasa ya kai miliyan 19.66 a jiya Asabar, rana ta farko na hutun kwanaki 5 na watan Mayu.
Wannan adadi ya kai matsayin koli a bangaren yawan tafiye-tafiya a rana daya. Wasu alkaluma da aka fitar da farko, sun yi hasashen Sinawa za su yi tafiye-tafiye ta jirgin kasa kimanin miliyan 120 a cikin kasar, daga ranar 27 ga wata zuwa 4 ga watan Mayu.
Karuwar tafiye tafiye na kara bunkasa bangaren yawon bude ido. Hukumar kula da yawon bude ido ta kasar Sin ta yi kiyasin za a yi tafiye-tafiye miliyan 240 domin yawon bude ido a lokacin hutun, inda ake ganin zai iya kaiwa matakin na 2019, wato kafin barkewar annobar COVID-19.
Bugu da kari, ana sa ran bangaren yawon bude ido ya samu kudin shigar da yawansa ya zarce yuan biliyan 120, kwatankwacin dala biliyan 17.4. (Fa’iza Mustapha)