A yau Laraba, hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin ta sanar da cewa, masana’antar fina-finai ta kasar ta kafa sabon tarihi yayin hutun Bikin Bazara na 2025, inda kudin tikitin kallon fina-finai da aka samu daga ranar 28 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Fabrairu, ya kai yuan biliyan 9.51, kwatankwacin dala biliyan 1.33.
Haka kuma, adadin masu zuwa kallon fina-finai ya karu, inda mutane miliyan 187 suka je dakunan nuna fina-finai yayin hutun, lamarin da ya kawo gagarumin ci gaba a bangaren sayen tikiti da ma yawan masu zuwa kallon fina-finai.
- Duk Wanda Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani, Shi Ma Sai An Hukunta Shi – Gwamna Sule
- ‘Yansanda Sun Cafke Baƙin Haure 165, An Miƙa Wa Hukumar NIS A Kebbi
Fim din da ya zama ja gaba shi ne na “Ne Zha 2”, wanda ya samu kimanin yuan biliyan 4.84.
A cewar dandalin Maoyan mai bada bayanan fina-finai, sauran fina-finan da suke kan gaba daga matsayi na 2 zuwa na 6 sun hada da “Detective Chinatown 1900,” da “Creation of the Gods II: Demon Force,” da “Legends of the Condor Heroes: The Gallants,” da “Boonie Bears: Future Reborn,” da kuma “Operation Hadal.”
Ban da haka kuma, an watsa wadannan fina-finai a wasu kasashe da yankunan duniya, inda suka samu yabo daga masu kallo. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp