Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a daren ranar Litinin sun kai hari a ofishin gudanarwar sakatariyar karamar hukumar Okehi a Jihar Kogi.
Ma’aikatun gudanarwa na sakatariyar karamar hukumar na daura da ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) na karamar hukumar.
- BUK Ta Kori Dalibai 27, Ta Dakatar Da 8 Kan Satar Jarabawa
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan IPOB 3, Sun Kama 2 A Anambra
Ko da yake ba a samu asarar rai ba, an ce ginin ya ruguje yayin da aka lalata wasu kayayyaki masu daraja a harin da aka kai da misalin karfe 9 na daren ranar Litinin.
Kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar Okehi Hon. Abdulraheem Ohiare, ya ci tura don tabbatar da faruwar harin
Har ila yau, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Oworo da ke bayan Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a ranar Litinin.
Sun kashe mutane da dama yayin da wasu suka jikkata a harin da aka kai da yammacin ranar Litinin.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shigo unguwar ne da misalin karfe 5 na yamma inda suka fara harbe-harbe kai tsaye.
Rundunar ‘yansandan Jihar Kogi, ba ta mayar da martani kan faruwar lamarin ba, duk da cewa an tura jami’an bincike zuwa wurin.