Ministan Muhalli, Balarabe Abbas Lawal, ya bayyana cewa Ma’aikatar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin da suka dace wajen rage ambaliyar ruwa a ƙasar.
Balarabe ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin yayin da yake karɓar Kwamitin Ad-hoc na Majalisar Wakilai kan Ambaliyar Ruwa, wanda Shugabansa Hon. Dr. Mandala Usman ya jagoranta tare da wasu ƴan kwamitin.
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum Uku A Zariya
- Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Yaya Da Ƙannuwa Da Wasu A Zaria
Ministan ya jaddada cewa ambaliyar ruwa lamari ne mai ɗaukar hankali, abin damuwa, kuma sau da yawa ana haddasa ambaliyar ne ta hannun mutum, wanda ke buƙatar haɗin kansa don samo mafita mai ɗorewa a sauƙaƙe.
Ya lura cewa Ma’aikatar ta aiwatar da manufofi da dama don hanawa da sarrafa ambaliyar ruwa da ke addabar al’ummomi da dama a faɗin ƙasa, waɗanda suka haɗa da:
Shirin dasa itatuwa (Afforestation Programme)
Dokar Tsabtace Amfani da Wuta ta Ƙasa. Dokar Gyara Yanayi ta Ƙasa. Hanzarta Ba da gargaɗi. Wayar da kan jama’a kan haɗarin ambaliyar ruwa. Tilasta dokokin muhalli. Horarwa da sabunta ƙwarewar jami’ai ƙwararru. Shigar da kayan aiki na zamani, da sauransu.
Har ila yau, ya bayyana cewa za a iya sarrafa ambaliyar ruwa ta hanyoyi kamar:
Taruwar ruwan sama (rain harɓest) kamar yadda ake yi a China. Gyara da gina ƙarin madatsun ruwa (dams). Kafa hanyoyin ruwa. Kafa ƙarin ɗakunan gwaje-gwaje kan ambaliyar ruwa. Haramta amfani da roba ɗaya-ɗaya (single plastic use).
Kulawa akai-akai da tsarin magudanan ruwa a faɗin ƙasa. Gudanar da ruwa (water management)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp