Shugaban Hukumar Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya amince ya koma kan mukaminsa, bayan da ya yi murabus a ranar Juma’a.
Wannan ya biyo bayan zaman sansanci da aka yi tsakanin gwamnan da Sheikh Daurawa, tare da wasu malamai a daren Litinin.
- Sin: Kalaman Da Amurka Ta Yi Wata Alama Ce Ta Siyasantar Da Harkokin Tattalin Arziki Da Cinikayya
- Ramadan: Sarkin Kano Ya Roƙi ‘Yan Kasuwa Da Su Taimaka Su Rage Farashin Kayan Abinci
Tun da farko rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin Kano tana ta daukar matakan tabbatar da an yi sulhu tun bayan da aka samu sabanin.
Wata majiya ta kusa da lamarin ta ce kakakin majalisar dokokin jihar, Jibril Falgore da babban limamin masallacin Babban Tarayya, Abuja Sheikh Ibrahim Maqari na daga cikin wadanda gwamnatin jihar ta tura wajen malamin don yin sulhu.
Daga baya gwamnatin ta aike tawaga daga zauren malaman Kano don bai wa Daurawa hakuri.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya soki yadda ake gudanar da aikin hukumar Hisbah.
Biyo bayan haka ne Sheikh Daurawa ya ajiye aikinsa a kasa da sa’o’i 24 da kalaman da gwamnan ya yi a bainar jama’a.