A yayin da ake shirye-shiryen jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, an tura jami’an tsaro masu yawa jihar Katsina, musamman a hanyar da ta taso daga birnin Katsina zuwa Daura.
Jami’an ‘yansanda da na sojojin Nijeriya sun bazu ko’ina a manyan wurare domin tabbatar da tsaro da tsari yayin da ake shirin jana’izar da ake sa ran za ta samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen Nijeriya.
- DA ƊUMI-ƊUMI: An Ɗage Jana’izar Buhari Zuwa Gobe Talata A Mahaifarsa Ta Daura, Jihar Katsina
- Rasuwar Buhari: Na Yi Rashin Ɗan’uwa, Aboki, Ɗan Ƙasa Nagari —Babangida
Tuni mutane da dama, ciki har da ‘yan uwa da abokan arziki, suka fara isa Daura domin yin bankwana da marigayi Janaral Buhari.
A fadar Sarkin Daura, an ga yanayi na jimami da damuwa a fuskokin mutane da dama, wanda hakan ya nuna irin girman rashi da aka yi a garin na Daura. Duk da cewa mutane na ci gaba da zuwa, garin Daura ya kasance cikin natsuwa, yayin da mazauna garin ke harkokinsu na yau da kullum a ƙarƙashin kulawar jami’an tsaro.
Mataimakin gwamnan Katsina, Faruk Lawal Jobe, na daga cikin manyan jami’an gwamnati na farko da suka isa Daura a safiyar Litinin. Haka kuma, an ga Sulaiman Amani, aboki na kusa ga Buhari, yana karɓar gaisuwar ta’aziyya a gidan marigayin.
An takaita yawan mutane da ke shiga gidan Buhari a Daura, yayin da ake ci gaba da shirya jana’izar da za a yi a ranar Talata. Tsaro ya kara tsananta a unguwar, yayin da iyalai da jami’ai ke shirye-shiryen binne mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ana sa ran karɓar ƙarin wasu manyan baki daga sassa daban-daban na duniya da za su isa Daura kafin lokacin jana’izar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp