An tsinci gawar wata ɗalibar aji ɗaya ta Jami’ar Taraba da ke Jalingo (TSU), a ranar Juma’a a cikin ɗakin saurayinta, lamarin da ya tayar da hankali jama’a a jami’ar.
Ɗalibar mai suna Comfort Jimtop, ’yar ƙaramar hukumar Takum ce, kuma tana karantar fannin koyon aikin jarida.
- Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok
- Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi
An gano gawarta da rana, inda aka samu kwalaben giya a kusa da gadon da ta kwanta.
Gidan da abin ya faru na da mazauna 15 ciki har da saurayinta, Emmanuel Shata.
Rahotanni sun ce bayan an gano gawarta, dukkanin mazauna gidan suka tsere.
Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Taraba, ASP Leshen James, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce suna neman saurayin tare da sauran mazauna gidan da suka tsere.
“Lokacin da jami’anmu suka isa wajen, ba kowa a cikin gidan. Saurayin da sauran mazauna gidan sun riga sun gudu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ’yansanda za su gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru da Comfort.
Lamarin ya haifar da firgici da damuwa ga ɗalibai da mazauna yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp