Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta ce an gano gawar mutum 9 da wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Shugaban Hukumar bayar da agaji ta (NSEMA), Alhaji Salihu Garba, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da manema Labarai a Minna ranar Lahadi.
- Hatsarin Kwale-kwale Ya Yi Sanadin Rasuwar Mutum 2 A Jihar Neja
- Kifewar Kwale-kwale Na Ci Gaba Da Salwantar Da Rayukan ‘Yan Nijeriya
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum goma a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.
Kazalika, rahotannin sun bayyana cewa wadanda abin ya rutsa da su ‘yan kasuwa ne, suna jigilar kaya ne daga unguwar Zongoru da ke yankin Bassa zuwa Gijiwa kusa da kasuwar Juma’a da ke Kuta, hedikwatar karamar hukumar Shiroro.
Akalla mutum 34 ne suke cikin jirgin wanda 10 daga cikinsu suka rasa rayukansu, yayin da aka kubutar da mutum 22.
Garba ya bayyana sunayen wadanda suka rasu, sun hada da Farida Muntari da Sharhabila Sagir da Bubakar Sadiq da Na’ima Ibrahim da Amina da Safaratu Ibrahim da Sadiq Ibrahim da kuma Rafiya Yakubu.
Ya ce har yanzu hukumar ba ta tantance biyu daga cikin mutanen da suka mutu ba, ya kara da cewa dukkan wadanda suka mutu ‘yan garin Zangoro ne.
Garba ya ce, akwai maza da mata manya 24 da kuma yara maza da mata 10 a cikin jirgin a lokacin da ya kife.
Garba ya kuma ce ana ci gaba da bincike don gano sauran gawarwakin.