An tsinci gawar wata mace mai suna Blessing John a dakin wani otel da ke kan titin Benin a Sabon Garin Zariya a jihar Kaduna.
An rahoto cewa, otel din na daya daga cikin wuraren da ake sauke mata masu zaman kansu don kama haya ta wucin gadi.
Wani mazauni a kusa da otel din wanda ya bukaci a sayakaya sunansa, yace ana zargin matar wani abokin harkallar ta ne ya kashe ta bayan kwana biyu kafin a gano gawarta da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar lahadi.
Majiyar ta ce, anji wani wari na fitowa daga dakin, inda lamarin ya ja hankalin jama’a aka gayyato jami’an ‘yansanda suka zo suka balle kofar dakin sika fito da gawawarta suka kai dakin ajiye gawarwaki na Asibitin koyarwa na ABU da ke Zaria.
Rahotanni sun ce, matar ‘yar asalin jihar Benuwai ce amma tana zaune ne a garin Zaria don yin karuwanci.
Sai dai an rahoto cewa, tuni jami’an ‘yansanda suka cafke mai kula da otel din domin gudanar da bincike.