Yanzu haka, an kara tura manyan injuna domin gudanar da aikin ceto a wurin da zaftarewar kasa ta auku a lardin Sichaun na kasar Sin. Da farko za su kwashe duwatsu da kasa da suka lullube wurin, kuma da zarar an ga alamun gini, za a sanar da ma’aikatan dake wurin domin kara bincike.
Zuwa karfe 11:00 na safiyar yau agogon Beijing, an tabbatar da kasa ta binne gidaje 10 da wata masana’ata 1, sanadiyyar zaftarewar kasar, wadda ta auku a gundumar Junlian ta birnin Yibin na lardin Sichuan. Haka kuma, mutum 1 ya rasa ransa yayin da 28 suka bata. Zuwa yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da aikin ceto. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)