Gwamna Babagana Zulum na Borno a ranar Lahadi ya mika ma Shehun Dikwa Ibrahim El-Kanemi sandar mulki a wani biki da ya gudana a garin Dikwa.
Ibrahim Ibn Umar El-Kanemi ya zama Shehun Dikwa na 13 bayan rasuwar marigayi sarki Mohammed Ibn Shehu Masta II wanda ya rasu a shekarar 2017.
- Haƙar Ma’adanai Na Sa Yara Ficewa Daga Makaranta A Jos
- Babbar Gasar Wasannin Kankara Ta Zama Damar Tabbatarwa Duniya Niyyar Karfafa Zaman Lafiya
A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya yabawa tsarin zaman lafiya da lumana da aka gudanar wanda ya kai zaben sabon Shehun Dikwa, inda ya bayyana cewa, hakan na nuni da yadda masarautar ke mutunta al’ada da bin doka da oda.
“Zaben Alhaji Ibrahim Ibn Umar El-Kanemi, a matsayin sabon Shehun Dikwa, an gudanar da shi cikin lumana da hadin kai wanda sarakunan masarautar suka taka rawar gani wajen zakulo wanda ya dace,” in ji Zulum.
Ya bukaci sarkin da ya yi ba da jagoranci daidai da irin kalubalen zamani, yana mai jaddada rawar da masarautar ke takawa wajen farfado da Borno daga shekaru masu yawa na rashin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp