Madaba’ar tattara bayanai da fassara ta kasar Sin, ta wallafa littafi game da bayanan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi don gane da shawarar ziri daya da hanya daya ko BRI, bugun harshen Turanci na shekarar 2023.
Wata sanarwar hukuma da aka fitar a Lahadin nan, ta ce za a rarraba littafin a sassan cikin kasar Sin da ma kasashen waje.
Sanarwar ta kara da cewa, ana fatan wallafar za ta taimakawa masu karatu na kasashen ketare, da damar kara fahimtar ma’ana, da matakai, da manufofi, da nasarorin da shawarar BRI ta cimma, kana hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar ta BRI. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp