Yayin da sabuwar shekara ta gargajiyar kasar Sin ke kara gabatowa, shirye-shiryen bidiyo na tallata shagalin murnar bikin bazara da babban rukunin gidan radiyo da talbijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya tsara, sun yi nasarar sauka a wurare da dama a duniya, inda suka gayyaci masu kallo na duk fadin duniya don kallon shagalin murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiyar kasar ta Sin, wato shekarar Zomo.
A karo na farko, an nuna shirin bidiyo na tallata shagalin murnar bikin bazara a wasu manyan birane biyar na kasar Amurka, ciki har da New York da Washington da dai sauransu.
Baya ga haka, CMG ya gabatar da bikin kunna fitilu masu kyan-gani har shekaru hudu a jere a husumiyar Burj Khalifa, dake zama shahararren gini mafi tsayi a duniya, da kuma gabatar da bidiyon tallata shagalin murnar bikin bazara har shekaru 3 a jere a filin jiragen saman kasa da kasa na Dubai, da ma wasu shahararrun wurare na duniya, wanda ya ja hankalin jama’ar wurin da masu yawon bude ido don tsayawa da kallo da kuma nishadantuwa da al’adun gargajiyar kasar Sin.
A yayin bikin bazara kuma, CMG zai gudanar da wasu ayyukan da suka shafi murnar sabuwar shekarar gargajiyar kasar ta Sin a hedkwatar MDD dake New York, da Moscow da ma Afirka ta kudu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)