Tsohon shugaban ‘yan jarida (NUJ) na kasa reshan Jihar Kano, Malam Abbas Ibrahim da mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya, Kwamired Kabiru Ado Maga Minjibri, sun ya ba wa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II, kan nada Alhaji Auwalu Mudi Yakasai a matsayin Dan Malikin Kano.
Sabon Dan Malikin ya kasance abokin gwagwarmayarsu ne a NLC da NUJ, kamar yadda suka bayyana ga manema labarai a wajen nadin nasa.
- Sin Ba Za Ta Canza Matsayarta Game Da Mayar Da Hankali Kan Kasashe Masu Tasowa Ba
- Gwamnatin Tarayya Da Google Sun Bullo Da Hanyar Samar Wa Da Matasa 2,500 Aikin Dogaro Da Kai
Malam Abbas ya ce Sarki Sunusi ya zabi wanda ya dace da wannan sarauta ta Dan Maliki, wanda ya kasance daya daga cikin hakimai a fadar masarautar Kano.
Shi ma mataimakin shugaban kungiyar kwadago na kasa, Kabiru ya ce babu shakka Sarkin Sanusi ya karrama su da babbar sarauta, kuma hakan zai kawo ci gaba mai yawa a masarautar Kano, wanda akwai bukatar masarautun kasar nan su yi koyi da Sarki Sanusi.
A nasa jawabin, Dan Malikin Kano, Alhaji Auwalu ya ce su a matsayinsu na zurri’ar gidan Dabo da Sarki Tukur da sauran sarakuna, wannan sarauta ta dade da barin gidansu, amma gashi Sarki Sunusi ya dawo musu da ita, abun a yaba masa ne.
Su ma ma’aikatan kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano (KNAPOLY), karkashin shugabancin Dakta Abubakar Umar Faruk, sun yaba wa Sarki Sunusi kan nada magatakardan kwalejin, Alhaji Mukhtar Ibrahim Bello, a matsayin Falakin Kano.