Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai yi magana ne a kan kurajen gaba:
- NSCDC Ta Cafke Hatsabibin ÆŠan Bindiga A Kano
- Kungiyar Masu Masana’antu Ta Samu Bashin Naira Biliyan 75 Daga Bankin BOI
Kuraje al’aura wani irin cuta ko matsala ce da ke damun fatar al’aurar dan’Adam mace ko namiji. Kamar yadda ku ka sani ne kalar kurajen ja ne, sannan wani lokacin ya kan hada da yi wa mutum zafi ko kaikayi tare da dan kunburi a dai-dai in da yake fitowa mutum. Idan mutum ya kamu da duk wata cutar kuraje wacca bai san da irinta ba, ya yi kokari ya garzaya zuwa wurin likita domin ya duba lafiyarsa.
Abubuwa da ke janyo kurajen al’aura daga cututtuka da ake kamuwa da su musamman a bandaki
Wadannan cututtukan a kan kamu da su ta hanyar jima’i ko kuma ta matsalar rashin isashen karfin sinadarin kariya a jikin dan’Adama wato ‘Autoimmune disorders’.
Ga kadan daga cikin.
Abubuwa da ke kawo kaikayi ko kuraje a jikin fatar al’aura:
1. Cutar kaikayin al’aurar mace (Baginal Yeast Infection) :
Irin wadannan kurajen ya kan addabi mata ne a al’aurarsu musamman idan suna da wata matsalar ciwon sanyi, yana sa kaikayi, ya kansa fata ta yi ja, ya kansa fatar gaba ya kwaye sannan ya kan sa mace ta rika fitar da wani irin farin ruwa gabanta.
2. Cutar Molluscum Contagiosum
Wannan cutar ta kan addabi fatar mutum, kurajen kan fito kananun zagayayyun kuraje a al’uarar dan’Adam, wani sa’in su kan yi kaikayi sannan kuma da yi wa mutum zafi.
3. Cutar balantis:
Wannan ya kan fito ne a fatar al’aurar namiji abin da ya kan kawo irin wannan cutar shi ne rashin tsabta, yana kawo kaikayi, ya kan sa fatar wurin ya yi ja dadewarsa na saka al’aura ta fid da wani irin farin ruwa.