Wata kotun majistare a Jos ta yanke hukuncin shekara ɗaya a gidan yari ga wani matashi mai shekara 23, bayan ya amsa laifin satar waya da kuma amfani da kuɗin wani daga asusun ajiyarsa ba tare da izini ba.
Mai shari’a Shawomi Bokkos ne ya yanke hukuncin bayan Iliya ya amsa laifinsa, inda aka yanke masa watanni shida a gidan yari ko kuma zabin biyan tarar Naira 20,000. Haka kuma, za a buƙaci ya biya diyya ta Naira 23,000 ga mai karar, ko kuma ya kara shafe wasu watanni shida a kurkuku.
Mai gabatar da kara, Sufeto Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa wanda aka yi karar, ya kai rahoto ranar 13 ga Agusta a ofishin ’yan sanda na “C” Division. Gokwat ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kutsa kai cikin gidan Musa inda ya sace wayarsa mai darajar Naira 20,000 sannan ya yi amfani da ita wajen karɓar rancen Naira 2,000 daga asusun ajiyar mai ƙarar.
Wannan laifi ya saba da dokokin Penal Code na Jihar Filato.