Wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam a Saudiyya sun ce wata kotun hukunta manyan laifuka a kasar ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin daurin shekarar 50 a gidan yari saboda kin ficewa daga yankin da za a yi aikin gina wani katafaren birnin mai cike da fasahar zamani na duniya wanda ake yi wa lakabi da Neom project.
Aikin na Neom project dai wani gagarumnin aiki ne da zai lakume kusan dala biliyan 500 da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ke jagoranta.
- Korona Ta Kusa Zama Tarihi A Duniya Baki Daya – WHO
- Ya Shiga Hannun ‘Yansanda Bayan Sayan Bindiga Don Kashe Mahaifansa
Masu gwagwarmaya sun ce an yanke wa mutanen biyu Abd -al-Ilah al-Huwaiti da Abdullah Dakheel al-Huwaiti – wadanda ‘yan uwan juna ne – hukuncin ne saboda bayar da goyon baya ga ‘yan uwansu wadanda suka ki yarda su fice daga yankin.
An kuma haramta musu tafiye-tafiye na tsawon shekara 50
An dai ruwaito cewa mutanen biyu ‘yan uwa ne ga Abd-al-Raheem al-Huwaiti, wanda jami’an tsaron kasar suka kashe saboda kin yadda ya fice daga yankin a shekarar 2020