Mahukunta a Jamhuriyar Nijar, sun ce ambaliyar ruwa ta kashe mutum fiye da 130 a kasar tun daga watan Yulin shekarar da muke ciki.
Nijar dai na fuskantar ambaliyar ruwa a duk shekara, to amma a bana adadin ya rubanya na bara.
- Korona Ta Kusa Zama Tarihi A Duniya Baki Daya – WHO
- Xi Jinping Ya Yi Ziyarar Aiki A Uzbekistan Tare Da Halartar Taron SCO
Kazalika ambaliyar ruwan ta kuma kashe dabbobi da dama da kuma lalata gonaki.
Talla
Ministan ayyukan jin kai na kasar, Lawan Magaji, ya ce yankunan Maradi da Zinder da kuma Diffa ne ambaliyar ta fi shafa.
Haka kuma ambaliyar ruwan ta tursasa wa mutane fiye da 150 barin muhallansu a wadannan yankunan.
Ambaliyar ruwan bana dai ta shafi kasashen yammacin Afirka da dama ciki har da Najeriya.
Talla