A ranar Litinin ne wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekaru 22, Najibullah Alkasim, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe maƙwabcinsa, Isyaku Ya’u, a lokacin wata takaddama a shekarar 2024.
Alkaliya Farida Dabappa, wacce ta yanke hukuncin, ta yanke hukuncin cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin kisan kai ga wanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba.
- Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin Lakurawa, An Harbe Ɗaya A Kebbi
- Jakadan Bangladesh Ya Yaba Wa MAAUN, Ya Buƙaci A Kafa Reshen Jami’ar A Ƙasarsa
Ta yanke hukuncin cewa, Alkasim ne ya yi sanadiyyar mutuwar wanda aka kashe da gangan ta hanyar daɓa masa sukundireba a ƙirji.
“Na yanke wa Alkasim hukuncin kisa ta hanyar ratayewa saboda daɓa wa mamacin sukundireba da ta yi sanadin mutuwarsa,” in ji Alkaliya.
Lauyan masu gabatar da kara, Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotun cewa, lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Janairu, 2024, a garin Dawakin Dakata, Kano.














