A yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mao Ning, ta yi bayani kan gudunmowar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) ta kasar Sin ta samar, a fannin rage talauci a duniya.
A cewarta, cikin shekaru 10 da suka wuce, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, ta janyo jari da yawansu ya kusan kaiwa dalar Amurka biliyan dubu 1, ga kasashen da suka rungumi shawarar, gami da fitar da mutane miliyan 40 daga kangin talauci.
Ban da haka, hadin gwiwar da ake yi a fannin aikin gona, karkashin shawarar, ya samar da karin abinci ga mutane masu bukata. Kana jarin da aka zuba a bangaren masana’antu, da aikin gina kayayyakin more rayuwa, sun samar da dimbin guraben aikin yi, duk a karkashin laimar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. (Bello Wang)