Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da ya ci gaba da hutun watanni uku kafin ya yi ritaya kamar yadda dokar ma’aikatan gwamnati (PSR) ta tanadar daga Oktoba 18, 2023, wanda zai yinl ritaya daga aiki a ranar 17 ga Janairu, 2024.
Don haka shugaban ya amince da nadin Alhaji Jalal Ahmad Arabi a matsayin sabon shugaban hukumar NAHCON na tsawon shekaru hudu a matakin farko.
- Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da ‘Ya’Ya 2 Na Dan Majalisar Dokokin Jihar Kwara
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a daren ranar Talata, wanda ya bayyana ci gaban, ta ce sabon shugaban NAHCON zai fara aiki a matsayin mukaddashinta a ranar 18 ga watan Oktoba, 2023.
“Shugaban kasa yana sa ran sabbin shugabannin NAHCON za su yi aiki cikin tsoron Allah tare da kiyaye ka’idojin aiki kamar yadda Alkur’ani mai girma ya tanada,” in ji Ngelale.