A ranar Asabar 4/5/2024 Sarkin Lafian Bare-bari tsohon mai Shari’a, Sidi Bage Muhammad, ya gudanar da gagarumin taron bikin murnar cika shekaru biyar kan karagar mulkin masarautar Lafiyan Bare-bari ta jihar Nasarawa.
Taron da ya samu halartar manyan sarakuna daga kowane sassa a fadin Nijariya.
- Gwamatin Tarayya Ta Fito Da Tsarin Cin Gajiyar Ma’adanan da Ke Jihar Nasarawa
- Karancin Wuta: Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Bai Wa AEDC Makonni 2 Don Gyara Wutar Lantarki
Da yake jawabi a wurin taron, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya ce, wannan taron ya nuna wa duniya cewa sarakuna suna kokari wajan tabbatar da Nijariya a matsayinta na dunkulalliyar kasa.
Sultan ya ce, a wannan taron sarakuna daga sassa daban-daban na Nijariya sun halarta domin nuna farin ciki da tabbatar da zaman lafiyar Nijariya.
Surkin Musulmi ya ce, sau da yawa mutane suna zagin shugabanni su ce basa yin aikin komai, alhalin lokacin da ake aikin mutane can suna barci.
Sultan yayi kira ga ‘yan Nijariya da su dage da yi wa shugabanni addu’ar kwarai domin samun ci gaban Nijariya.
Shi ma a nasa jawabin, Shehun Borno, Ibin Umar Abubakar El-Kanami, ya yi fatan Allah ya kara hada kan yan Nijariya ya budawa kowa a hanyar sana’arsa.
Ya bukaci al’umma da su zama masu taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri wajen fallasa ‘yan ta’adda a duk inda suke.
Gwamnan jihar Nasarawa. Abdullahi Sule, ya godewa dukkanin sarakuna da suka baro jihohinsu suka zo Jihar Nasarawa don halartar wannan taro.
Bayan kammala taron manyan baki sun shiga cikin fada domin bude gidan tarihi na jerin sarakuna sha bakwai da suka mulki masarautar Lafiyan Bare-bari wanda Sarki Sidi Bage Muhammad ya gina.