Yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke yi a kasar Tajikistan, a yau Juma’a, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya shirya bikin cudanyar al’adun Sin da Tajikistan, mai taken “Kaddamar da sabon zamani na sada zumunta” a birnin Dushanbe, fadar mulkin kasar Tajikistan. Kana an sanar da kaddamarwar aikin ziyara, da intabiyu da ma’aikatan wasu kafofin yada labaru na kasashen 2 za su yi a kasar ta Sin, duk a wajen bikin.
Shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi a wajen bikin, inda ya ce CMG na son karfafa cudanya tare da abokan hulda na kasar Tajikistan, musamman ma a fannin raya al’adu, don karfafa zumuntar dake tsakanin kasashen 2. (Bello Wang)