Sabon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, mai ra’ayin kawo sauyi, ya sanar da dubban magoya bayansa da suka hallarci bikin rantsar da shi a Brasilia babban birnin kasar, cewa babban aikin da ke gabansa shi ne na hada kan ‘yan kasar.
BBC ta rawaito cewa, Shugaba Lula ya ce wagegen gibin da ke tsakanin attajirai da matalautan kasar ya zama karfen-kafa ga tsarin dimokradiyya, sannan ya lashi takobin yin mulki domin kowane dan kasar ya amfana.
- 2023: Atiku Zai Bude Iyakokin Nijeriya Bayan Ya Lashe Zabe – Tambuwal
- SERAP Ta Maka Wike, Okowa Da Wasu A Kotu Kan Badakalar Naira Biliyan 625
Bayan da aka kammala bikin rantsar da shi, Shugaba Lula ya shaida wa majalisar kasar Brazil cewa zai sake gina kasar daga matakin da ya kira na matsanancin lalacewa, musamman ma dajin nan na Amazon – duka karkashin matsalolin da ya gada daga Jair Bolsonaro.
Shugaba Lula ke nan ke cewa “Alhakin kulawa da dajin amazon da ma wuraren da dumbin albarkatun karkashin kasa suke kamar karfe da man fetur da tarin ruwan ruwan dadi da ke bulbulowa daga karkashin kasa da kuma hanyoyin samar da hasken lantarki wadanda ba sa gurbata muhalli.”
Ya kuma ce, “Tun da muna da ‘yan cin kai da sanin ya kamata, za mu bar dukkan mutanen duniya su amfana da wadannan albarkatun.”
(Backanno) Ya ce salon mulkin tsohon shugaba Bolsonaro ya keta sauran zaman lafiyar da ‘yan kasar ke amfana da shi – kuma ya ce kin amincewa ya sha kaye a babban zaben kasar zai raba ‘yan kasar ne kawa.
Shugaba Lula ya lashe zabe na wa’adin mulkinsa na uku ne bayan da wata kotu ta yi watsi da wani hukunci da aka yanke masa kan cin hanci da rashawa.